21 Satumba 2024 - 11:39
Ayatullah Safayi Bushehri: Sojojin Jamhuriyar Musulunci Suna Da Manyan Kayan Aikin Soji A Dukkan Bangarori Na Karfin Kariya + Hotuna

Ayatullah Safayi Bushehri ya jaddada cewa: Ko a halin yanzu sojojin Jamhuriyar Musulunci suna da iko mai girma da yawa na soji a dukkan bangarori na lissafin bangaren karfin tsaro.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti As - ABNA ya habarta cewa: Ayatullah Safayi Bushehri, wakilin jagora a lardin Bushehr a safiyar yau a wajen faretin da sojojin kasar suka yi bisa zagayowar ranar farko ta makon tsaro mai alfarma ya bayyana cewa: Daya daga cikin muhimman abubuwan da wata kasa ya yakamata tana da shi shi ne ce ikon karfinta na rundunonin soji a duk fannoni na tsaro.

Ya kara da cewa: A duk lokacin da wata kasa ke da wannan bangaren na karfi to kuma take da matsayi na musamman a tsarin tsaro da na'urorin tsaro na duniya, to zai zamo kasar tana da ikon kasa da kasa.

Ayatullah Safayi Bushehri ya jaddada cewa: Ko a halin yanzu sojojin Jamhuriyar Musulunci suna da iko mai girma da yawa na soji a dukkan bangarori na lissafin bangaren karfin tsaro.